Harin kunar bakin wake a Yemen ranar Sallah

Yemen na fuskantar hare-hare daga bangarori daban-daban

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yemen na fuskantar hare-hare daga bangarori daban-daban

A kalla sojojin Yemen 10 ne suka mutu a wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan wani sansanin dakarun tsaro kusa da filin jirgin sama na Aden.

Haka kuma 'yan bindiga sun dirarwa babbar hedikwatar tsaro a yankin Khormaksar, da ke Kudancin birnin Aden mai tashar jiragen ruwa, inda suka bude wuta.

Har yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma kungiyoyin IS da al-Qaeda sun sha kai irin wadannan hare-hare a baya.

Aden nan ne inda gwamnati Yemen take.

Saudiyya da dakarun da ke goyon bayan gwamnati na ta fafutukar ganin sun kwace iko a babban birnin kasar Sanaa daga hannun 'yan tawayen Houthi.