Birtaniya ta zargi Amurka kan Iraqi

Jagoran binciken John Chilcot Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Amurka ta jagoranci yakin Iraqi a shekarar 2003.

Manyan jami'an gwamnatin Burtaniya da ke sahun gaba a matakin da kasar ta dauka na shiga kawancen yakin da Amurka ta jagoranta a kasar Iraqi sun dora alhakin abubuwan da suka faru kan Amurkar.

A jiya Laraba ne dai John Chilcot ya gabatar da zazzafan rahoton, kan yadda aka shirya kai hare-hare, da abubuwan da suka biyo bayan yakin da aka yi a shekarar 2003.

Wani Janal din sojin Burtaniya Janal Tim Cross da ke sahun gaba a shirya yadda yakin zai kasance, ya ce Amurka ta daidaita sojojin Iraqi da jam'iyyar Ba'ath ta kasar ba tare da yin shawara da kowa ba.

Da yake jawabi a Amman, mai shiga tsakani kan batun na Iraqi Saleh Mutlaq, yace yakin Iraqi shi ya sake sharewa ayyukan ta'addanci hanya.

Mutlaq ya kara da cewa sakamakon mamaye Iraqi da aka yi, da yakin da ya biyo baya wanda babu komai a ciki face koma baya da aka samu, shi ne ya janyo karuwar ayyukan ta'addanci da ake fuskanta a halin yanzu.

A yau duniya na fuskantar barazana saboda an kassara Iraqi.