Ana cin zarafin mutane a Kamaru — Amnesty

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amnesty na zargin dakarun tsaron Kamaru da cin zarafin bil'adama

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International za ta kaddamar da sabon rahoto a kan cin zarafin dan adam da ta ce hukumomi da dakarun tsaron Kamaru ke yi, a yakin da suke da kungiyar Boko Haram.

Rahoton mai taken ''Right cause, wrong'' na kunshe da bayanai kan yadda dakarun tsaro ke take hakkin dan adam da rashin adalci a yakin da kasar ke yi na kokarin kare fararen hula daga munanan hare-haren Boko Haram.

Rahoton ya ce an tsare daruruwan mutane da ake zarginsu da goyon bayan Boko Haram, ba tare da isassun hujjoji ba.

An tsare yawanci mutanen ana gana musu azaba.

A ranar 14 ga watan Yuli ne za a kaddamar da rahoton a Yawunde babban birnin Kamaru.

Kamaru dai na daga cikin kasashen da ke fama da matsalar kungiyar Boko Haram.