An yanke hukunci kan yakin Rwanda

Kokon kawunan wadanda aka kashe a yakin Rwanda Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Har yanzu radadin abinda ya faru a shekarar 1994 na zukatan al'umar kasar.

Wata kotu a kasar Faransa ta yankewa tsaffin shugabannin al'umar Rwanda hukuncin daurin rai da rai, bisa hannun da suke da shi a kisan kare dangin da aka yi a kasar shekarar 1994.

Octavio Ngenzi shi ne magajin garin Kabarondo, ya yin da Tito Barahira shi ne zai gaje shi, a jari'ar da aka dade ana yi, an samu mutanen biyu da laifin cin zarafin bil'adama, da taimakawa kitsa kisan kiyashin yawancin 'yan kabilar Tutsi a kauyen Kabarondo da ke gabashin Rwanda a watan Aprilun shekarar 1994.

A yaki mafi muni da kasar ta fuskanta dai, daruruwan maza da mata da kananan yara aka kona lokacin da suka nemi mafaka a wata Majami'a da ke kauyen na Kobarondo.

Wannan shi ne karo na biyu da ake yanke hukunci akan wadanda suke da hannu a yakin na Rwanda, shekaru biyu da suka gabata ne aka yankewa wani jami'in hukumar leken asirin kasar hukunci duk dai a kasar ta Faransa.