An kai hari kan 'yan Shi'a a Iraq

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A farkon makonnan nan ne aka kashe wasu 'yan Shi'ar kusan 300

Jami'ai a kasar Iraqi sun ce akalla mutum 30 ne suka rasa ransu sannan da dama suka jikkata sakamakon harin da aka kai a taron mabiya mazhabar Shi'a a Baghdad.

Wasu 'yan kunar-bakin-wake tare da 'yan bindiga ne dai suka kai harin.

Maharan sun tayar da bam a dab da kofar shiga wuri mai tsarki da mabiya Shi'ar suke bukukuwan Sallar Idi a garin Balad da ke arewacin Baghdad, babban birnin kasar Iraqi.

Bayan nan kuma 'yan bindiga da dama sun bude wuta a kan masu ibadar kuma daga bisani wasu 'yan bindigar suka tashi bama-baman da ke jikinsu.

Wannan harin ya faru ne kasa da mako guda bayan bayan da kusan 'yan Shi'a 300 suka mutu a wani harin bam mafi muni a birnin na Baghdaza.