Alhinin rasuwar Umaru Shinkafi

Hakkin mallakar hoto NO CREDIT
Image caption Umaru Shinkafi ya yi fice a harkokin siyasa da leken asiri a Nijeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu manyan 'yan siyasa da masu fada-a-ji na kasar sun bayyana alhininsu na rasuwar Alhaji Umaru Shinkafi.

Alhaji Umaru Shinkafi, wanda ya rasu a wani asibiti na kasar Biritaniya ranar Laraba, ya yi fice a harkokin leken asiri da siyasar Najeriya.

Ya rike mukamai da dama, ciki har da Babban Daraktan hukumar leken asiri a lokacin mulkin Alhaji Sehu Shagari, wanda shi ne ma rahotanni suka ambato yana sanar da shugaban kasar cewa za a yi juyin mulki amma tsohon shugaban kasar bai dauki mataki ba.

Marafan na Sokoto ya kuma shiga takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar NRC a shekarar 1992.

Kazalika ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasar a karkashin gamayyar jam'iyyun APP/AD inda Olu Falae da shi suka fafata da Cif Olusegun Obasanjo/Atiku Abubakar a zaben shekarar 1999.

A wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya Femi Adesina ya aikewa manema labarai, shugaban ya bayyana Alhaji Umaru Shinkafi a matsayin mutumin da ya taka muhimmiyar rawa wajen dawowar kasar kan turbar mulkin dimokradiyya.

Shi ma tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abukar, ya ce Alhaji Umaru Shinkafi na "Daya daga cikin 'yan siyasa masu hazaka da sanin ya kamata."

Sun yi rokon Allah ya jikan sa.

Alhaji Umaru Shinkafi ya bar mata uku da 'ya'ya biyar, cikin su har da Hajiya Zainab Atiku, mai dakin gwamnan jihar Kebbi da Hajiya Hadiza Yari, mai dakin gwamnan jihar Zamfara.