"Buhari ya saba alkawari "- BBOG

Kungiyar da ke fafutukar ceto 'yan matan Chibok, wato Bring Back Our Girls ta nuna rashin jin dadi game da abin da ta bayyana da rashin cika alkawura daga bangaren shugaban kasar, Muhammadu Buhari, shekara guda bayan ganawarsa da mambobin kungiyar.

A wani taron manema labaru a Abuja, kungiyar ta ce rashin cika alkawuran da shugaban kasar ya dauka babban koma-baya ne a fafutikar da ake yi ta kubutar da mutanen da mayakan Boko Haram suka sace.

Hajiya Aisha Yesufu, daya daga cikin shugabannin kungiyar ta shedawa BBC cewa za su nemi sake ganawa da Shugaba Buhari dan nuna masa rashin jin dadin su dangane da rashin cika alakawuran:

A ranar 8 ga watan Yulin bara ne dai wasu mambobin kungiyar suka gana da shugaba Muhammadu Buhari, inda suka gabatar masa da shawarwari kan batutuwan da suka shafi kubutar da 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace.