Boko Haram ta kai hari a Damboa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana yin amfani da mata domin kai hare-haren kunar-bakin-wake

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe akalla mutum shida a harin da suka kai a garin Damboa na jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce 'yan kunar-bakin-wake ne suka tashi bama-baman da ke jikinsu a wani masallaci da ke garin na Damboa ranar Juma'a da safe.

Girman harin ya sa masallacin ya rushe gaba daya.

Mutane da dama kuma sun jikkata sakamakon harin.

Harin kunar-bakin-wake dai ba bakon abu ba ne a Najeriya, musamman yadda 'yan Boko Haram kan yi amfani da kananan yara mata domin kai hare-haren.