Wani mutum zai sha dauri a Kano

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Kano na Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekara 30 a gidan yari ga wani Bafulatani makiyayi.

Kotun ta samu mutumin mai suna Dahiru Abdullahi ne da laifin fasa-kwaurin kananan makamai da albarusai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya.

Kotun ta daure mutumin ne ba tare da zabin tara ba.

Hukumar tsaron farin kaya ta SSS ce ta gurfanar da Dahiru a gaban kotun, bayan kama shi a ranar tara ga watan Mayun 2015 a garin Pambegua a cikin jihar Kaduna.

Da yake jawabi kafin karanto hukuncin, alkalin kotun mai shari'ah J.K Omotosho ya ce daga cikin shaidun da aka gabatar a gaban kotun, jami'an hukumar tsaron farin-kaya ta Najeriya sun kama bafulatanin wanda kuma ya ce yana sana'ar tukin mota, bayan samun bayanan sirri kan yadda yake fasa-kwaurin makamai.

An tuhumi Dahiru da mallakar kananan bindigogi kirar pistol guda uku da alburusai 1, 337 da wasu alburusai 929, inda aka fafake kasan motarsa aka boye su.

Dahiru Abdullahi, wanda ya kare kansa a gaban kotu, ya ce shi direba ne kuma wasu fasinjansa ne suka dora masa kaya domin ya kai musu wani wuri.