Koriya ta arewa ta sake harba makami mai linzami

Hakkin mallakar hoto KCNA

Sojojin Koriya ta kudu sun ce Koriya ta arewa ta yi biris da takunkumin kasa da kasar da aka kakaba mata, ta harba wani abu mai kama da makami-mai-linzami daga wani sansanin sojinta na ruwa.

Ta dai harba wannan makamin ne kwana guda bayan Amurka ta cimma wata yarjejeniyar da Koriya ta kudu domin girka wata garkuwa ko na'urar kakkabe makami mai linzami a kasar Koriya ta kudun.

Kasashe biyun sun cimma yarjejeniyar girka na'urar ne sakamakon gwaje-gwajen makami mai linzamin da Koriya ta arewa ta yi a farkon wannan shekarar.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa koriya ta arewa ta yi gargadin cewa, za ta rufe duk wasu hanyoyin diplomasiyya da Amurka, har sai an janye takunkumin.

A watan Junairun daya gabata ne koriya ta arewa ta yi gwajin makami mai linzami karo na hudu, inda ta yi da'awar cewa shi ne na farko da aka yi amfani da makamin da ake iya harba wa daga ruwa.

Dan lokaci kalilan bayan nan, sai kasar ta kaddamar da tauraron dan adam, wanda ake gani a matsayin gwaji na makamin linzami mai dogon zango.