An kama mutanen da suka kai hari a Masallacin Annabi

Hakkin mallakar hoto SAP
Image caption Daya daga cikin mutanen da aka kama yana shan miyagun kwayoyi.

Hukumomi a kasar Saudiyya sun ce mutum 12 cikin 19 da aka kama bisa zargin hare-hare uku da aka kai a kasar ranar Litinin 'yan kasar Pakistan ne.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ya ce wani dan kasar mai suna Naer Muslim Hamad ne ya kai hari a kusa da Masallacin Annabi Muhammad (SAW), lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum hudu.

Ya kara da cewa matashin, mai shekara 26, yana amfani da miyagun kwayoyi.

An kuma bayyana sunayen mutum uku da suka kai hari a Qatif, kodayake ba a san kasar da suka fito ba.

Mutanen su ne: Abdulrahman al-Omar (23), Ibrahim al-Omar (20) da Abdulkarim al-Husni (20).

Ma'aikatar harkokin gidan ta ce babu daya daga cikin mutanen da ke rike da katin shaidar zama a cikin kasar.

Hare-haren da aka kai a Qatif sun faru ne a rana daya da wadanda aka kai na harin kunar-bakin-wake a Madina.

Kazalika wani mutum ya mutu a Jeddah ranar Litinin a lokacin da ya yi yunkurin tayar da bama-baman da ke jikinsa.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren, sai dai ana zargin kungiyar da ke ikirarin yin jihadi ta IS da hannu a kai su.