Tsugunne ba ta kare ba a Amurka

Amurkawa sun ci gaba da zanga-zangar Allah-wadai da kisan da 'yan sanda ke yi wa bakar-fata a kasar, duk kuwa da kiran da Shugaba Obama ya yi ga al'umomin kasar cewa su hada kansu, bayan wani dan bindiga ya harbe wasu 'yan sanda biyar a Dallas.

Galibin zanga-zangar dai ta lumana ce, inda mutane ke furta wasu kalamai suna cewa "ran bakar-fata na da daraja", kodayake wasu masu zanga-zangar sun kara da 'yan sanda a jihar Louisiana da Minnesota.

Tun da farko dai shugaba Obama ya musanta cewa sabuwar kyamar launin-fatar da ta kunna-kai a Amurka ta yi muni irin na wani zamani da aka yi a wajejen 1960 da 'yan kai:

Ya ce ina da yakinin cewa kan Amurkawa bai rarraba kamar yadda wasu suka zata ba.

Hakika zukatan dukkan jinsin Amurkawa sun dugunzuma da wannan harin ba gaira ba dalili da ake kai wa 'yan sanda.