An kori jami'an diflomasiyar Amurka daga Rasha

Image caption Shugaba Putin na Rasha da Obama na Amurka

Rasha ta ce ta kori jami'an diflomasiya biyu na Amurka daga kasar a watan jiya, a matsayin ramuko ga kora mata nata biyu gida da Washington ta yi.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Ryabkov, ya ce daya daga cikin jami'an da Rasha ta kora, ya yi dauki ba dadi da wani mai gadi a wajen ofishin jakadancin Amurka a dake Moscow.

Rasha ta ce jami'in diflomasiyyar ya bugi mai gadin a fuska da gwiwar hannu.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ta ce mai gadin ne ya farwa jami'in na ta haka nan siddan.

A watan Yuni ne Amurka ta kori jami'an diflomasiyyar Rasha biyu saboda wannan lamari.

Amurka na zargin Rasha da daure gindin cin zarafin jami'an diflomasiyyar Amurka da iyalansu a Moscow.