Bujumi ya kashe mai hawan kaho

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani Bujumi ya yi sanadin mutuwar wani kwararren mai wasan hawan kaho a Spaniya ko Andalus, kuma wannan ne karon farko da Sa ya halaka dan wasa a wannan karnin.

Dan wasan hawan kahon mai suna Victor Barrio ya mutu ne yana da shekara 29 a duniya, kuma Bujumin ya huda shi ne da kaho a kirji, ana tsakiyar wasa a gaban dubun-duabatar 'yan kallo, a garin Teruel da ke gabashin kasar, kuma an nuna wasan kai-tsaye ta gidan talabijin.

Rahotanni dai sun za a kashe Bujumin, mai suna Lorenzo.

Wasan hawan kaho dai na daga cikin al'adun kasar Spaniya, wadda al'umarta ke alfahari da shi.

A bangare guda kuma, masu rajin kare hakkin dabbobi na adawa da wasan, suna cewa rashin imani ne da ya kamata a haramta shi.