An rufe tashar da Zakir Naik ke wa'azi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mutane sun yi zanga-zangar nuna adawa da wannan mataki

Gwamnatin Bangladesh ta ce za ta hana wata fitacciyar tashar talbijin ta Musulunci, Peace TV yada shirye-shiryenta a kasar.

Hakan na zuwa ne a lokacin da tashar da saka wa'azin wani fitaccen Malami Zakir Naik, wanda ake zargin wa'azin ne ya tunzura masu tayar da kayar bayan da suka kashe mutum 22 a wani hari da suka kai kantin shan shayi a Dhaka, babban birnin kasar.

Sai dai Mista Naik ya musanta wannan zargi.

Ita ma gwamnatin Indiya ta dauki matakin hana kallon tashar a kasarta.

A wani matakin na daban kuma, gwamnatin Bangladesh ta yi kira ga makarantun sakandire da na gaba da su da su sanar da hukumomi a duk lokacin da wani dalibi ya yi fashin zuwa makaranta na fiye da kwana 10.

A makon da ya gabata ne wasu mahara suka kai hari wani kantin shan shayi har suka kashe mutane 22 a birnin na Dhaka.