An watsa wa mata uku asid a Afghanistan

A Kabul babban birnin Afghanistan, wasu mata uku na ci gaba da samun sauki, bayan wasu maza sun watsa musu ruwan asid mai kona fata.

Kunar da daya daga cikin matan, wacce ake yiwa magani a asibiti, ta samu ta yi muni sosai.

Ba kasafai ake samun irin wannan hari na ruwan asid a Kabul ba, kuma har yanzu ba a gano dalilin maharan ba.

A wasu kasashen nahiyar Asia, a wasu lokuta, wasu kan yi amfani da asid a matsayin makami, musanman akan mata.

Shekaru takwas da suka gabata, wasu maza a kudancin Afghanistan sun watsa wa wani ayarin mata 'yan makaranta ruwan asid.

Ana zargin mazan 'yan kungiyar Taliban ne da suke adawa da karatun 'ya'ya mata.