'Yan Boko Haram 'na neman mafaka a Lagos'

Image caption Rahotanni sun ce 'yan Boko Haram na neman mafaka a Kudancin Najeriya

Rahotanni sun ce mayakan da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne na neman mafaka a birnin Lagos da ke Kudo maso Yammacin Nigeria.

Wani mai aikin sa-kai da ya jagoranci samamen da aka kai kan wasu mutane, ya shaida wa BBC cewa, a ranar Lahadi sun kama mutane biyar da ake zargin 'yan Boko Haram ne.

Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta ce ba ta da masaniyar wannan kame da masu aikin sa-kan suka yi.

Amma a baya rundunar 'yan sandan ta ce 'yan Boko Haram na kwarara zuwa jihar daga Arewacin kasar.

Akalla mutane 20,000 suka mutu a shekaru bakwan da aka shafe ana rikicin na Boko Haram, yayin da wasu sama da miliyan biyu suka bar gidajensu.

A kwanakin baya Ko da a baya-bayan nan jami'an tsaro da wata kungiya mai sa ido a kan yaki da 'yan Boko Haram sun gano maboyar wasu da ake zargi 'yan kungiyar ta Boko Haram ne a Lagas, abin da ya kai ga kama wasu daga cikinsu.

Bincike ya nuna cewa mutanen na guduwa Kudancin kasar ne neman mafaka sakamakon matsin da suke fuskanta daga sojojin kasar a Arewa maso Gabas.

Sharhi, Umar Shehu Elleman, BBC Hausa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan Boko Haram na yin wannan kaura ne saboda matsin lambar da suke fuskanta daga sojoji

Bayanai na nuna cewa hadin gwiwar da ake samu tsakanin jami'an tsaro da kuma masu aikin sa kai don yaki da Boko Haram yasa ana ci gaba da kamasu a wuraren da suke buya a birnin Lagos.

Ma'aikacin sa-idon ya ce tuni aka mayar da mutanen zuwa birnin Maiduguri, na jihar Borno, amma bai bayar da bayanin wajen da aka mika su ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da masu aikin-sa-kai da jami'an tsaro suka yi irin wannan samame tare da kama wadanda ake zargi 'yan kungiyar ba ne.

Ba tun yanzu ba ake rade-radin cewa akwai 'yan Boko Haram a Lagos, sai dai ba su cika zuwa da makamai ba, sai dai don neman mafaka.