Za a yanke hukunci a kan tekun kudancin Sin

Hakkin mallakar hoto

Ana sa ran wani kwamitin sulhu zai yanke hukunci a kan wani yanki da ake takaddama a kansa da ke tekun kudancin Sin, wanda China ke ikirarin cewa yankinta ne.

Kasar Philippines ce dai ta gabatar da batun gaban kotun sasantawa da ke Hague, shekaru ukun da suka wuce, tana cewa matakin da China ta dauka na hana Philippines din gudanar da zirga-zirga a teku ya saba wa dokar kasa da kasa.

China dai ta juya wa kwamitin sasantawar baya, tana cewa ba huruminsa ba ne.

Batun da kwamitin zai duba zai maida hankali ne wajen rarrabbewa ko wasu abubuwan da ke yankin da aka takaddama a kansa za a dauke su a matsayin tsibirai ko tsaunuka.

China dai na kikirarin cewa mafi yawan tekun kudancin ta mallakinta ne, kuma Allah ya huwace wa yankin albarkatun kasa.

Wasu kasashen duniya dai ciki har da Malaysia da Vietnam na dakon jin yadda hukuncin zai kaya.