An rufe shafukan sada zumunta a Ethiopia

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Miliyoyin mutane ne ke amfani da shafukan sada zumunta a Afirka

Hukumomi a Ethiopia sun rufe shafukan sada zumunta da muhawara a lokacin da dalibai da ke gudanar da jarrabawar shiga jami'a.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ambato wani kakakin gwamnatin kasar na cewa an rufe shafukan ne domin "kada su dauke hankulan daliban."

An yi satar ansar wasu darussa inda aka wallafa su a shafukan intanet a watan jiya, lamarin da ya sa aka soke yin jarrabawarsu a lokacin.

AFP ya ce ba a iya shiga shafukan Facebook, Twitter, Instagram da kuma Viber tun daga ranar Asabar din da ta wuce.

Kakakin gwamnatin, Getachew Reda ya ce, "an rufe shafukan sada zumunta kuma sai ranar Laraba za a bude. Shafukan suna dauke hankulan dalibai."

Wani fitaccen mai fafutika a shafukan sada zumunta Daniel Berhane ya yi tur da wannan mataki.