Amurka ta bukaci Iran ta saki wasu fursunoni

Hakkin mallakar hoto rahana

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bukaci Iran da ta saki wani dan kasuwa Bafarisi dan asalin Amurka da wani Kwara, wadanda ke da zama a Washington, duk kuwa da rahotannin da ke cewa suna daga cikin wasu 'yan kasar waje hudu da Iran din ke tuhuma a cikin makonni biyun da suka wuce.

Babu dai cikakken bayani a kan ainihin laifin da ake tuhumarsu da aikatawa.

Sauran mutum biyun kuma sun hada da wani malamin makaranta Bafarisi dan asalin Iran da kuma wata mata Bafarisa 'yar asalin Burtaniya.

Tun a farkon wannan shekarar ne Kakakin ma'aikatar shara'ar Iran ya bayyana cewa ana zargin cewa 'yan kasar masu jinin wata kasa na aikin leken asiri a Iran.