Yaushe rabonku da ganawa da 'yan majalisun dokokinku?

A Najeriya, yanzu haka dai 'yan majalisar dokokin kasar suna hutu, kuma bisa tsari irin na dimokuradiyya kamata ya yi 'yan majalisar su yi amfani da wani …ďangare na wannan hutu wajen komawa mazabunsu domin jin koke-koken jama'arsu, tare da yi musu bayani a kan irin ayyukan da suka yi a majalisa.

To anya 'yan majalisar suna komawa mazabun nasu a irin wannan lokaci kuwa?

Wakilinmu a Kano Mukhtar Adamu Bawa ya zagaya birnin Kano domin jin ko jama'a suna ganin 'yan majalisar da suka zaba a irin wannan lokaci, ga abin da suke cewa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti