Nigeria: Masallaci na ƙulla aure a Abuja

A Najeriya, wani masallaci a Abuja babban birnin kasar, ya bullo da wata hanya ta haɗa auratayya tsakanin al'umma, kuma bisa wannan tsari dai ana ƙulla aure bayan an cika fom da kuma wasu sharuda na tantance maneman, kuma daga nan ne za a ba wa maza masu buƙatar auren izinin ganin wadda za su iya aura.

Tuni dai Masallacin ya yi nasarar hada aure da dama ta wannan hanyar.

Abdou Halilou ya yi hira da Malam Hamisu Alheri Dumkawa, ladanin masallacin juma'a na FCDA a Abuja, wanda kuma shi ne ke jagorantar wannan shiri.

Ya soma ne da yin karin bayani a kan yadda wannan tsari ya samo asali:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti