An nemi a tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An yi kira ga bangarorin biyu su tsagaita wuta

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya bukaci shugabannin siyasa a Sudan ta kudu da su tsawatar wa sojojinsu, bayan sabon rikicin da ya barke a Juba, babban birnin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Kwamitin sulhin ya nuna damuwa dangane da hare-haren da aka kai kan ofishinsa da kuma sansanonin masu gudun hijira da ke kasar, yana cewa hare-haren ka iya zama laifukan yaki, kasancewarsu barazana ga rayuwar farar-hular da suka fake a ciki.

Shantal Persaud ita ce jami'ar da ke kula da ofisihin, kuma ta ce "babban aikinmu shi ne kare farar-hula, kuma muna da masu gudun-hijira kusan mutum dubu 170 a sansanoninmu shida da ke fadin kasar.

Fadan dai ya kaure ne tsakanin sojojin da ke goyon bayan shugaban kasar Salva Kiir da masu goyon bayan mataimakinsa, Riek Machar, kuma ana fargabar cewa kasar na iya sake fadawa yakin basasa.

An yi amannar cewa sama da mutum 200 ne suka mutu tun da rikici ya barke ranar Juma'a.