Faɗa ya sake ɓarkewa a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rikici yana kara kamari a Sudan Ta Kudu duk da yarjejeniyar zaman lafiya ta 2015

Tashin hankali ya sake barkewa a Sudan ta Kudu tsakanin dakarun da ke goyon bayan shugaban kasar da kuma mataimakinsa.

Wani dan jarida a Juba, babban birnin kasar, ya shaida wa BBC cewa ana jin karar fashewar bama-bamai a birnin, inda ake amfani da manyan bindigogi.

Rahotanni sun ce fiye da mutum 200 aka kashe a fadan da ya barke tun ranar Juma'a.

Wannan na faruwa ne sa'o'i kadan bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga bangarorin da ke fadan da su kawo karshen tashin hankalin.

Mene ne ya haifar da fadan?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tsohon Jakadan Najeriya a kasar Sudan, Dahiru Sulaiman, ya shaida wa BBC cewa za a dade kafin a shawo kan rikicin na Sudan ta Kudu, wacce ta samu 'yancin kai a shekarar 2011.

Ya ce zaman doya-da-manja tsakanin Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar, da kabilanci, da rashin adalcin shugabanni, shi ne musabbabin rikicin.

Wannan fada dai ya sanya tsoro kan barkewar wani sabon rikici, da alamar cewa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2015 za ta rushe.