Mikiya ta so ɗauke yaro a Australia

Hakkin mallakar hoto Christine OConnell Instagram 55chris
Image caption Yaron ya yi ta faman tsala ihu a lokacin da mikiyar ta wafto shi

Wata katuwar mikiya ta yi kokarin dauke wani yaro a wajen wani shahararren baje-kolin dabbobi da ake dauka a talbijin a kasar Australiya.

Dumbin mutanen da suka taru a wajen baje-kolin na kallon lokacin da mikiyar ta sanya kafufunta a kan yaron wanda yake tsala kuka, a kokarinta na waftarsa.

Ganau sun ce mikiyar ta yi kokarin dauke yaron ne tamkar yadda take daukar kaji.

Yaron, mai kusan shekara takwas, ya tsira amma mikiyar ta ji masa ciwo a fuskarsa.

Wata mata da aka yi abin a kan idonta Christine O'Connell, ta shaida wa BBC cewa, mikiyar ta sheko da gudu ne daga nisan kusan kilomita 15, inda kai tsaye ta durfafo yaron don waftarsa.

Ba tare da bata lokaci ba aka dakatar da daukar shirin a talbijin.

Wannan al'amari ya faru ne ranar Laraba, 6 ga watan Yuli a gandun naman daji na Alice Springs Desert Park.