Za mu kakkaɓe ɓarayin shanu — Buhari

Image caption 'Yan fashi na dauke da miyagun makamai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai wata ziyara a jihar Zamfara da ke arewa-maso-yammacin kasar.

A lokacin ziyarar, shugaba Buhari zai kaddamar da wata sabuwar rundunar yaki da 'yan fashin shanu da suka addabi yankin inda ya ce gwamnatinsa ta daura damarar fatattakar 'yan fashin shanu da suka addabi jama'a.

Daruruwan mutane ke mutuwa a kowace shekara a jihar sakamakon hare-haren da 'yan fashin masu dauke da muggan makamai ke kai wa a kauyukan jihar.

Wannan dai na zuwa ne 'yan makonni bayan da wani tsohon dan majalisar dattawan kasar daga jihar ya yi kira ga shugaban kasar da ya ayyana dokar-ta-ɓaci a jihar har sai tsaro ya inganta.