Amurka za ta ba da shaida kan 'neman karuwai'

Hakkin mallakar hoto national assembly
Image caption Mista Entwistle ya ce yana da hujjoji kan zargin da ya yi

Majalisar wakilan Najeriya ta gayyaci jakadan Amurka a kasar ya bayyana a gabanta domin yin karin bayani kan zargin da ya yi wa wasu mambobinta na bigewa da neman karuwai yayin wata ziyarar aiki a kasar.

A watan da ya gabata ne James Entwistle ya aike wa shugaban majalisar wakilan, Yakubu Dogara, ya zargi 'yan majalisa uku daga cikin goma da suka kai ziyara kasar da nuna rashin kamala da yunkurin yin fyade da neman karuwai.

A cewar Mista Entwistle 'yan majalisar su ne: Mohammed Garba Gololo (APC, Bauchi), Samuel Ikon (PDP, Akwa Ibom) da kuma Mark Gbillah (APC, Benue), zargin da suka musanta.

Ya kara da cewa Mohammed Garba Gololo ya yi yunkurin rungumar wata ma'aikaciya da ta je gyara masa dakinsa da zummar yin lalata da ita.

"Mark Terseer Gbillah da Samuel Ikon sun bukaci ma'aikatan wurin ajiye motoci na otal din da su nemo musu karuwai," a cewar Mista Entwistle.

'Ba a gayyaci otel din ba'

Tun a wancan lokacin ne dai 'yan majalisar suka musanta zargin, inda suka ce a shirye suke su koma Amurka domin kare kansu.

Kazalika, 'yan majalisar sun bukaci jakadan Amurka ya janye zargin ko kuma su shigar da kararsa a kotu.

Lamarin dai ya sa majalisar ta kafa kwamitin bincike, wanda ya nemi Mista Entwistle ya bayyana a gabansa domin gabatar da hujjojinsa kan zarge-zargen da ya yi.

Mai magana da yawun kakakin majalisar Turaki Hassan ya shaida wa BBC cewa a ranar Alhamis ne ake sa ran Mista Entwistle zai bayyana a gaban kwamitin.

Shugaban kwamitin da'a na majalisar Nicholas Ossai, ya ce ba su gayyaci jami'an otal din da aka yi zargin 'yan majalisar sun nemi karuwan a cikinsa ba, yana mai cewa gayyatar da suka yi wa Mista Entwistle ta wadatar.