Sanatoci sun yi 'barazanar tsige Buhari'

Buhari da Saraki Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Dangantaka ta yi tsami tsakanin Bukola Saraki da Buhari

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa wasu 'yan majalisar dattawan Nigeria sun yi barazanar tsige Shugaba Muhammadu Buhari idan har ba a janye tuhumar da ake yi wa shugabannin majalisar ba.

A wani zama na sirri mai cike da rudani a yammacin ranar Talata, an kuma nemi Sanata Kabiru Marafa da Suleiman Hunkuyi, da su janye zargin yin dokokin jabu kan shugabannin majalisar.

Shugaban majalisar Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu, na fuskantar shari'a kan amfani da dokokin boge wurin zabarsu.

Duka mutanen biyu sun musanta zargin, inda suka ce siyace kawai.

Majiyarmu ta ce wasu sanatoci sun sha alwashin sa kafar wando daya da duk wanda ya nemi kawo cikas ga shugabancin Bukola Saraki.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Buhari ya musanta cewa wasu ne ke juya shi

Rahotanni sun ce an yi hayaniya sosai a zaman da aka yi, wanda Sanata Saraki ya jagoranta, inda aka rinka sa-in-sa tsakanin masu adawa da kuma goyon bayan shugabannin majalisar.

Wasu sanatoci sun kuma yi barazanar sanya sufeto janar na 'yan sanda ya kama ministan shari'a na kasar idan bai amsa gayyatar da suka yi masa ba.

Wani kwamitin majalisar ne ya gayyaci Abubakar Malami (SAN) domin ya yi bayani kan karar da ya shigar kan Bukola Saraki da Ekweramadu a gaban wata kotun Abuja.

Masu sharhi na ganin wannan batu zai kara zafafa rashin jituwar da ke tsakanin bangaren shugaban kasa da majalisar, wacce ta dade da yin tsami.

Kawo yanzu babu wani bayani a hukumance daga majalisar kan zaman na ranar Talata, wanda aka yi a cikin sirri.

Hakazalika babu wani martani daga fadar Shugaba Buhari.