An fara tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ba a ji karar harbe-hareb a birnin Juba ba

Da alama yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, bayan an kwashe kwana uku ana mummunan barin-wuta tsakanin dakarun da ke goyon bayan Shugaba Salva Kiir da Mataimakinsa Riek Machar.

Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Birnin na Juba ya yi tsit, kuma babu rahotannin shawagin jiragen yaki masu saukar ungulu ko tankokin yaki a kan hanyoyin birnin.

Ranar Litinin ne dai Salva Kiir da Riek Machar suka sanar da cewa za su tsagaita wuta, wacce ta fara aiki da misalin karfe uku a agogon Najeriya da Nijar.

Taho-mu-gamar da aka yi tsakanin bangarorin biyu tana barazana ga yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla.

A shekarar 2011 ne Sudan ta Kudu ta zama kasa mai cin gashin kanta daga Sudan, bayan an kwashe shekara da shekaru ana yakin-basasa.