An ba da belin shugaban 'yan hamayyar Uganda

Image caption Kizza Besigye ya shafe fiye da wata biyu a tsare a kurkuku bisa zargin cin amanar kasa

Wata kotu a Uganda ta bayar da belin babban jagoran 'yan hamayyar kasar, Kizza Besigye, bayan ya shafe fiye da wata biyu a tsare a kurkuku bisa zargin cin amanar kasa.

An dai kama shi ne bayan ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar, sannan ya sha rantsuwar kama aiki bayan zaben shugaban kasar da aka yi a watan Fabrairu mai cike da ce-ce-ku-ce.

An sanya masa sharudan bayar da beli cikin su har da bayar da $30,000 da kuma daina zanga-zanga da addu'o'in mako-mako da magoya bayan jam'iyyarsa ke yi a hedikwatar jam'iyyar.

Mista Besigye ya yi alamar cin nasara a lokacin da yake barin harabar kotun, yana mai cewa ya yi farin cikin fita daga kurkuku.