Theresa May za ta sha rantsuwar kama aiki

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A ranar Larabar nan ne Firai ministan Biritaniya, David Cameron zai mika ragama ga sabuwar shugabar jam'iyyar Conservative Theresa May.

Mista Cameron zai bar mukamin ne bayan shafe shekaru shida, amma zai ci gaba da wakiltar mazabar sa a majalisar dokokin Birtaniya.

Tuni dai ya kwashe kayan sa daga fadar Downing street.

Theresa May 'yar shekara 59 yanzu za ta zama mace ta biyu da ta rike matsayin Firai ministar Biritaniya.

Za ta karbi ragamar a daidai lokacin da kasar ke fuskantar manyan kalubale tun bayan kuri'ar raba gardama da ta amince kasar ta fice daga kungiyar tarayyar Turai.