An kashe tsohuwar ma'aikaciyar BBC

Image caption Hafsa Mossi tsohuwar ma'aikaciyar BBC Swahili ce

Wasu 'yan bindiga sun harbe wata tsohuwar minista har lahira a Bujumbura, babban birnin kasar Burundi.

Hafsa Mossi dai 'yar majalisa ce a majalisar dokoki a Burundi, kuma tsohuwar ma'aikaciyar BBC Swahili ce.

An samu karuwar rikice-rikice a Burundi tunda Mista Nkurunziza ya bayyana cewa zai kara tsayawa takara a karo na uku.

Kashe-kashen dai na zuwa ne a daidai lokacin da tattaunawar sulhun da ake yi a kan rikicin Burundi a kasar Tanzania ke fuskantar kalubale .

Jami'an gwamnati sun yi watsi da bayyanar mambobin 'yan hamayya wanda hakan ya dakatar da cigaban yarjejeniyar.