Dole masu shirin aure su yi gwaji a Anambra

Ana haifar yara da dama dauke da cutar sikila a Nigeria

A kokarin kawar da cutar amosanin jini (wato ciwon sikila), gwamnatin jihar Anambra da ke kudancin Nigeria ta fara bin matakin tilasta wa namiji da mace yin gwajin jini, kafin a daura musu aure.

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne sabo da cutar na ci gaba da zama babbar matsala ga rayuwar al'ummar Najeiya.

Gwamnatin jihar ta yi barazanar hukunta wadanda suka ki bin dokar.

Wani mataimaki na musamman ga gwamnan jihar ta Anambara Mr. James Eze, ya shaida wa BBC cewa gwmnatin za ta samar da wata doka da za ta tabatar da cewa namiji da mace da suke shirin aure sun kai kan su gwajin jini kafin a daura musu aure.

Ya ce hakan zai taimaka wajen rage yaran da ake haifa da larurar amosanin jini.

Masu fafutukar yaki da cutar dai a Najeriya sun yi maraba da wannan mataki na gwanatin Anambara, inda suka ce hakan shi ne matakin farko na dakile cutar. Kuma masu fafutukar sun yi fatan sauran jihohin kasar za su yi koyi da Anambara.

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen fama da matsalar cutar amosanin jini.