Ba za mu tsige Buhari ba - Sanatoci

Wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya sun musanta zargin da aka yi cewa suna shirin tsige shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Daya daga cikin 'yan majalisar da ake zargi da kitsa yunkurin tsige Shugaba Buhari, Sanata Dino Meyale, ya bayyana rahotannin da cewa na kanzon-kurege ne.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Mista Melaye ya ce "karya ake yi mana da aka ce muna shirin tsige Shugaba Buhari, kuma wadanda suka yi wannan zargi ba sa son zaman lafiyar Najeriya".

Ya kara da cewa hakan ba zai sanya shi da takwarorinsa su daina fafutikar da suke yi wajen tabbatuwar mulkin dimokradiyya ba.

A ranar Laraba ne dai wata majiya ta shaida wa BBC cewa wasu 'yan majalisar dattawan Nigeria sun yi barazanar tsige Shugaba Muhammadu Buhari idan har ba a janye tuhumar da ake yi wa shugabannin majalisar ba.

A wani zama na sirri mai cike da rudani a yammacin ranar Talata, an kuma nemi Sanata Kabiru Marafa da Suleiman Hunkuyi, da su janye zargin yin dokokin jabu kan shugabannin majalisar.

Shugaban majalisar Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu, na fuskantar shari'a kan amfani da dokokin boge wurin zabarsu. Duka mutanen biyu sun musanta zargin, inda suka ce siyace kawai.

Majiyarmu ta ce wasu sanatoci sun sha alwashin sa kafar wando daya da duk wanda ya nemi kawo cikas ga shugabancin Bukola Saraki.