Theresa May ta zama Firai Ministar Birtaniya

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Theresa May ta kama aiki a matsayin sabuwar Firai Ministar Birtaniya bayan da David Cameron ya yi murabus.

A yammacin ranar Laraba ne Sarauniya Elizabeth ta umarci Misis May ta kafa gwamnati bayan da Cameron ya shaida mata cewa ya bar kujerar.

A ranar Litinin ne aka zabi Misis May a matsayin shugabar jam'iyyar Conservative, bayan da Cameron ya yi murabus sakamakon kuri'ar da 'yan kasar suka jefa ta ficewa daga Tarayyar Turai.

Nan gaba kadan ne ake sa ran za ta bayyana sunayen mutanen da za su yi aiki a gwamnatin da za ta kafa.

Sabuwar Firai Ministar Birtaniya

1956

Ita ce shekarar da aka haifeta

1980

Ta auri Mista Philip May

  • 1997 Ta zama 'yar majalisar dokoki

  • 2010 Sakatariyar cikin gida

  • 2016 Firai Ministar Birtaniya

A jawabinta na farko ga 'yan kasar, Misis May ta ce, ''Burina shi ne na ga Birtaniya ta fi yadda take a yanzu.''

Ta kammala jawabin da cewa, ''Hakika za mu iya inganta Birtaniya fiye da yadda take yanzu idan har muka hada kai muka yi aiki tare.''

''Hadin kai don inganta Birtaniya, shi ne taken da za mu dinga ji a 'yan kwanaki masu zuwa,'' in ji sabuwar Firai ministar.

Tun da farko Mista Cameron ya halarci muhawarsa ta karshe a matsayin Firai Minista, inda 'yan majalisa suka jinjina masa kan rawar da ya taka.

A lokacin da yake jawabi ga manema labarai a kofar fadarsa, ya ce, zamowa Firai Minista ita ce "daukaka mafi girma da ya samu a rayuwarsa.''

Mista Cameron wanda ke tsaye tare da matarsa da 'ya'yansa uku, ya ce Birtaniya na cikin yanayi mai inganci fiye da lokacin da ya same ta.

Theresa May ta zamo mace ta biyu a tarihi da ta taba zamowa Firai Ministar Birtaniya bayan Margaret Thatcher a shekarar 1979.