'Yan fashin shanu sun addabi Kano

A Najeriya, wasu al'ummomi a jihar Kano na ci gaba da bayyana irin ukubar da suke fuskanta a hannun 'yan fashin shanu da suka addabe su.

Daruruwan mutane ne dai 'yan fashin shanun suka hallaka cikin 'yan shekarun nan a jihohin Kano da Zamfara da Kaduna dama wasu sassan kasar inda yanzu haka jama'a da ke zaune a wadannan yankuna ke rayuwa cikin fargaba.

Wakilinmu na Kano, Mukhtari Adamu Bawa ya ziyarci wani da irin wadannan 'yan fashi suka jikkata, kuma a yanzu haka yake kwance magashiyan a gadon asibiti:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A ranar Laraba ne dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kaddamar da wata rundunar yaƙi da 'yan fashin shanu a jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce yanzu haka jama'a da ke zaune a wadannan yankuna na rayuwa cikin fargaba.