BH: Yadda Maiduguri ta 'sauya'

Hakkin mallakar hoto Fatima Abubakar
Image caption Ba a jin wani labari mai dadi game da Maiduguri

Bayan an shafe shekara bakwai ana fama da rikicin kungiyar Boko Haram, mutane da dama wadanda hare-haren kungiyar suka shafa musamman 'yan birnin Maiduguri da ke Jihar Borno sun tsinci kansu a wani irin matsanancin hali.

A duniya baki daya, babu wani labari mai dadi da ake ji game da birnin, inda nan ne cibiyar kungiyar.

Fatima Abubakar, 'yar Maiduguri ce kuma tana daukar hotuna da kuma yin aikin bayar da agaji.

Ta shaida wa BBC cewa tana so ta yi amfani da hotunanta, wadanda take wallafawa a shafin Instagram, domin sanar da duniya cewa 'yan Maiduguri na rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Hakkin mallakar hoto Fatima Abubakar
Image caption Mutane da dama na rayuwa cikin kwanciyar hankali

Ta kara da cewa tana wallafa hotunan ne domin ta bayyana wa duniya irin sabuwar rayuwar da 'yan Maidugurin suke yi, sabanin irin labarun kisa da na fashewar bama-bamai da kuma na tashin hankali da kafafen yada labarai suke nunawa duniya.

Fatima ta ce wasu daga cikin irin hotunan da ta dauka su kan ba ta tausayi:

"Ina shiga damuwa matuka da labaran kananan yara wadanda suka rasa iyayensu a sakamakon hare-haren Boko Haram kuma hakan ya tirsasa musu yawo a kan titunan birnin."

Hakkin mallakar hoto Fatima Abubakar
Image caption Fatima tana wallafa hotunan a shafukan sada zumunta

Duk da dai cewa hotunan da Fatima take dauka suna tasiri, ta shaida wa BBC cewa tana fuskantar kalubale da dama.

"Mutane suna ganin cewar daukar hotunan da nake yi ya sabawa al'adarmu, inda wasu kuma suke cewa a matsayi na na mace, ya kamata na yi aure na zauna a gida, amma wadannan kalamai ba su taba kashe min gwiwa ba."

Hakkin mallakar hoto Fatima Abubakar
Image caption Suna rayuwarsu kamar yadda suka a baya

Fatima Abubakar ta kara da cewa duk da dai hare-haren Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 20,000 da tirsasawa sama da miliyan biyu barin muhallansu, ya karfafa dangantaka da tsoron Allah tsakanin iyalai da kuma 'yan uwa.

Ta ce zai dauki tsawon lokaci kafin wasu 'yan mazauna Maiduguri da suka yi gudun hijira su koma gidajensu.

Sai dai kuma akwai yakinin cewa da taimakon gwamnati da kuma soji, birnin da ake yi wa kirari da cibiyar kwanciyar hankali, zai koma kamar yadda aka san shi a baya.