Mota ta tattake mutane da dama a Faransa

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hukumomi a kasar Faransa sun ce mutum 84 ne suka mutu bayan wani hari da aka kai da babbar mota cikin taron jama'a a birnin Nice.

Kimanin mutum hamsin kuma sun jikkata, 18 daga cikin su ke cikin mawuyacin hali.

An yi kira da jama'a su bayar da gudunmuwar jini ga mutanen da harin na daren Juma'a ya rutsa da su.

Kananan yara da dama sun jikkata a harin, kuma an garzaya da su asibitoci domin ba su kulawa.

Iyalai da dama na ci gaba da neman 'yan uwansu da suka bace.

Image caption Sama da mutane 50 ne suka jikkata a harin na Faransa

Har safiyar Juma'ar nan ba a iya gano direban motar ba, amma an ga katin shaida na wani matashi dan kasar Faransa wanda kuma dan asalin kasar Tunisiya ne a cikin motar.

Rahotanni sun ce matashin, mai shekara 31 mazaunin birnin na Nice ne, sai dai ba a tabbaatar ba ko shi ne ya kai harin.

Wasu rahotanni sun ce an jiyo karar harbe harbe, ko da dai dama lamarin ya faru ne a lokacin da ake wasa da wuta a wani bangare na bikin na samun yancin kai.

Duniya ta yi tur da harin

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sergei Lavrov na Rasha da John Kerry na Amurka sun aza firanni a ofishin jakadancin Faransa da ke Moscow

Tuni wasu shugabannin kasahen duniya suka yi Allah-Wadai dsa harin.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana harin a matsayin wani dabbanci.

Shugaba Obama ya bayyana harin da wani al'amari mai munin gaske inda ya bayyana goyon bayan daukacin Amurkawa da al'ummar Faransa, daddiyar abokiyarta.

Shugaban Majalisar nahiyar turai Donald Tusk, ya ce abun takaici ne harin da aka kaiwa mutane lokacin da suke murnar samun 'yanci, inda ya ce daukacin al'ummar nahiyar turai dana Asiya na tare da jama'ar Faransa