Theresa May za ta nada ƙarin ministoci

Image caption Wasu daga cikin ministocin sun yi fafutikar ganin kasar ta fice daga Tarayyar Turai

A ranar Alhamis ne ake sa ran sabuwar Firai Ministar Biritaniya Theresa May za ta sanar da nadin karin wasu mukarraban gwamnatinta bayan da ta nada wasu fitattu masu goyon bayan ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai a matsayin ministoci.

Misis May ta nada Boris Johnson, jigo a fafutikar ficewar Biritaniya daga kungiyar Tarayyar Turai a matsayin ministan harkokin waje.

Mr Johnson, wanda shi ne tsohon magajin garin birnin London, ya ce yanzu Biritaniya na da damammaki na inganta dangantakarta da nahiyar turai da kuma sauran kasashen duniya.

Kazalika, an nada Philip Hammond a matsayin Wazirin Baitul-mali, yayin da Amber Rudd ta zama Sakatariyar cikin gida.

Misis May ta kuma nada David Davis a matsayin sabon sakataren da zai kula da shirin kasar na ficewa daga Tarayyar Turai.

A jawabinta na farko jim kadan bayan kama aiki, Misis May ta yi gargadin cewa yanzu an shiga wani yanayi ne na gagarumin sauyi a kasar.

Sai dai ta yi alkawarin cewa kasar za ta samar wa kanta sabuwar alkibla.

Sabuwar Firai Ministar Birtaniya

1956

Ita ce shekarar da aka haifeta

1980

Ta auri Mista Philip May

  • 1997 Ta zama 'yar majalisar dokoki

  • 2010 Sakatariyar cikin gida

  • 2016 Firai Ministar Birtaniya