Turkiya: An kama masu yunkurin juyin mulki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Erdogan ya ce masu juyin mulkin za su dandana kudar su

Hukumomin kasar Turkiya sun ce an kashe kwamandan sojojin da ya jagoranci yunkurin juyin mulkin da aka dakile.

Mai rikon mukamin shugaban sojojin kasar Janar Umit Dundar ya ce an kashe masu yunkurin juyin mulkin 104, yayin da aka kashe yan sanda da fararen hula 90, sannan wasu mutane 1,100 kuma sun jikkata.

Wani babban jami'in gwamnati ya ce an kama sojoji 1,500 da suka yi yunkurin juyin mulkin.

wasu gungun sojoji ne su ka yi yunkurin "kifar" da gwamnatin, bayan da tun da farko suka mamaye muhimman wurare a biranen Istanbul da Ankara.

Shugaba Racep Tayip Erdogan ya ce har yanzu gwamnatin sa ce ke da iko a kasar.

Rahotanni sun ce an kubutar da shugaban sojojin kasar Janar Hulusi Akar, wanda tun da farko masu yunkurin juyin mulkin suka yi garkuwa da shi.

Wani jami'in gwmnati yace an kama sojoji masu yunkurin juyin mulkin 750, cikin su har da janar janar biyar, da masu mukamin Kanal 29.

Wasu darururuwan sojojin sun ajiye makaman su sun kuma mika wuya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu sojoji sun mika wuya ga gwamnati

Hukumomin kasar sun ce an kashe mutane 60 a musayar wuta tsakanin masu yunkurin juyin mulkin da kuma yan sanda dake goyon bayan gwamnati, mafi yawan wadan da aka kashe din fararen hula ne.

Wasu gungun sojoji ne suka mamaye titunan biranen Ankara da Santanbul a daren Asabar, sannan suka bayar da sanarwa ta gidan talabijin na NTV cewa sun kwace iko da dukkan kasar.

Firai ministan kasar Mista Binli Yildirim ya ce gwamnati ba ta amince da matakin ba.

An dai kaddamar da yunkurin juyin mulkin ne a lokacin da shugaban kasar Racep Tayyip Erdogan ya tafi hutu, to sai dai bayan fara yunkurin na juyin mulki ya koma birnin Santanbul, inda magoya bayan sa suka yi daififi domin tarbara sa.

Wani dan jarida a birin Ankara yace mutane sun yi futar 'farin dango' kan tituna bayan Shugaba Erdogan ya yi kira a gare su su futo, a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban yan Turkiya sun yi dafifi domin taryar shugaba Erdogan

Tun gabanin komawar sa an yi hira da shi ta gidan talabijin inda ya yi kira ga magoya bayan sa su futo zanga zanga dan nuna goyon baya ga dimokradiyya.

Ya ce yunkurin juyin mulkin ba zai yi nasara ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Turkiya ba su goyi bayan juyin mulkin ba

Jama'a da dama dai sun futo kan tituna suna rike da totocin kasar inda suke nun adawa da yunkurin juyin mulkin.

A wasu lokutan ma jama'a sun inga jifan tankokin yaki na sojojin masu bore.

Hakkin mallakar hoto AFP

An bada rahoton cewa wani jirgi mai saukar Aungulu na soja ya yi harbi a kan gidan talabijin din kasar.

Jiragen yakin sojoji masu biyayya ga gwamnati sun harbo jirgi mai saukar ungulu daya, bayan firai ministan kasar ya ba su umarni.

An ji karar fashewar abubwa a birnin na Ankara.

Ana kuma samun rahotannin harbe-harben bindiga a Ankara, babban birnin kasar ta Turkiyya.

Har da safiyar Asabar din nan dai ana ci gaba da jin karar harbe harbe.

Amma daga baya l'amura sun lafa, inda sojoji da dama ke ci gaba da mika wuya.

Hakkin mallakar hoto epa