Za a kaddamar da fasfon bai daya na AU

Shugabannin Afirka na haduwa a Kigali, babban birnin Rwanda domin taron koli na kungiyar kasashen Afirka- AU.

Ana sa rai taron ya mayar da hankali kan rikicin Sudan ta Kudu da Burundi, da kuma kaddamar da fasfo na kungiyar ta AU.

Manufar fasfon na AU ita ce samar da yanayin zirga-zirgar jama'a ba takura, da bunkasa kasuwanci a tsakanin kasashen nahiyar.

Za a fara bayar da fasfon ne ga shugabannin kasashen Afirka da wasu manyan jami'an kungiyar AU, kuma ana sa rai, fara aiki da fasfon gadan-gadan zai dauki wasu shekaru.

Za kuma a zabi sabon shugaban kungiyar ta AU a wurin taron, domin shugabar mai ci, Nkosazana Dlamini-Zuma za ta sauka.