Australia na son kulla alaka da Birtaniya

Tutar Australia Hakkin mallakar hoto
Image caption Mista Turnbull na son karfafa dangantaka ne tsakanin kasashen biyu.

Firai Ministan Australia, Malcolm Turnbull ya bukaci Birtaniya ta kulla huldar ciniki ba tare da wani shinge ba da kasarsa, a lokacin da Birtaniyar ta zabi fita daga kungiyar Tarayyar Turai.

Mista Malcolm Turnbull ya ce yana bai wa batun muhimmanci kwarai da gaske.

Wakilin BBC ya ce, ''Wannan maganar kulla huldar cinikin za ta kara wa Firai ministar Birtaniya Theresa May, kwarin-gwiwa wadda ke da yakinin cewa Birtaniya za ta ci gajiyar ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai, ta hanyar kulla yarjejeniyar kasuwanci da manyan kasashen duniya.

Sai dai kuma Birtaniya ba ta da ikon kulla irin wannan yarjejeniyar sai ta kammala fita daga kungiyar Tarayyar Turai.