An kama mutane 5 bisa alaka da harin Nice

Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Bernard Cazeneuve ya ce akwai yiwuwar mutumin da ya tattake fiye da mutane tamanin da babbar mota a Nice, ya dauki tsattsaurar akida ce cikin dan kankanin lokaci.

Mista Cazeneuve ya ce harin na ranar Alhamis, ya nuna irin sabuwar barazana mai wuyar magance wa da kasar ke fuskanta.

Ya ce ya yi amanna, wasu mutane suna kai munanan hare hare ne a madadin kungiyar IS, duk da cewa ba kungiyar ce ta ba su horo ba.

Tun da farko, kungiyar IS ta ce daya daga cikin mabiyanta ne ya kai harin, saboda bukatar da ta yi mu su na kai hari kasashen dake yaki da ita a Iraki da Syria.

A halin yanzu kuma, 'yan sanda a Faransar sun kama mutane shida bisa alaka da harin na Nice.

Mutanen da suka mutu suna daga cikin cincirindon jama'a ne masu kallon wasa da wuta, lokacin da mutumin ya kutsa cikinsu da babbar motar.