Faransa ta kara matakan tsaro

Harin da aka kai birnin Nice Hakkin mallakar hoto .
Image caption Harin ya hallaka mutane da dama da jikkata wasu.

Gwamnatin kasar Faransa ta sake girke 'yan sandan kar ta kwana dubu goma sha biyu a birnin Nice, dan sake inganta tsaro bayan harin da aka kai.

Ministan cikin gidan Bernard Cazenueve, ya yi kira ga 'yan kasar su ma su shiga aikin da 'yan sandan za su yi, su fito kwan su da kwarkwatar su dan kare iyakokin kasar.

Gwamnatin Faransa dai na shan suka, saboda kai hare-hare guda uku kwarara da aka kai kasar cikin watanni goma sha takwas da wasu ke ganin ta gaza kare al'umar ta.

Mista Cazenueveya kira harin da aka kai ranar alhamis a birnin Nice da cewa wata babbar barazana ce da ta sake tunkaro kasar da zai yi wuya a shawo kan lamarin cikin takaitaccen lokaci.