An kashe ma'abociyar shafin zumunta a Pakistan

Image caption Qandeel Baloch

Jami'ai a Pakistan sun ce an yi wa wata fitacciyar ma'abociyar amfani da shafukan sada zumunta kisan gilla, a wani lamari da ake gani na dawo da martabar gidansu ne.

Qandeel Baloch, ta yi suna a wurin mutane da yawa a kasar wajen yada sakonni da hotuna da bidiyo, a wasu lokuta na batsa.

Ta sha bayyana kanta a matsayin mai rajin daga darajar mata, sai dai masu ra'ayin gargajiya sun yi Allah wadai da halayyarta.

Ta kasance a kanun labarai a 'yan kwanakin da suka wuce bayan ta yada hotunanta da wani fitaccen malami, Mufti Qavi, wanda mutuncinsa ya zube saboda haka.

'Yan sanda na zargin dan uwanta da kashe ta, ta hanyar shake mata wuya.