Turkawa sun nuna wa Erdogan goyon baya

Dubun-dubatar Turkawa na cigaba da bin titunan da ke manyan biranen Turkiyya, suna rera wakoki, rike da tutocin kasar don nuna goyon bayansu ga gwamnatinsu ta dimokradiyya.

Tun cikin dare dandalin da ke Istanbul ya yi cikar kwari da jama'a suna rera taken da ke cewa al'ummar kasar ba za ta bari sojoji su kwace mata kasa ko kuma su raba ta da mukin dimokradiyya ba.

Shugaban kasar, Recep Tayyip Erdogan, ya yi jawabi ga dandazon mogoya bayansa a wajen harabar majalisar dokoki da ke Ankara, babban birnin kasar, kuma majalisar dokokin na daga cikin wuraren da masu yunkurin juyin mulki suka mayar da hankali a kansu ranar Juma'a da daddare.

Shugaba Erdogan ya zargi wani Shehun Malami Baturke da ke Amurka mai suna Fethullah Gulen da hannu wajen kitsa yunkurin juyin mulkin, kana ya bukaci Amurka ta tisa keyarsa zuwa Turkiyya.

Sai dai Fethullah Gulen a nasa bangaren ya musanta zargin.