"Yunkurin juyin mulki yayi bakin tabo ga Turkiya"

Image caption Firayiministan Turkiya Binali Yildrim a tsakiya

FirayiMinistan Turkiya, Binali Yildrim ya bayyana yunkurin juyin mulki a kasar a matsayin bakin tabo ga demukradiyar kasar.

Ya ce mutane dari da sittin, akasarinsu fararen hula sun mutu a gwagwarmayar kwato wa kasarsu 'yanci.

Ya bayyana wadanda suke da hannu a yunkurin juyin mulkin a matsayin 'yan ta'adda da suka fi mayakan Kurdawa na PKK hadari.

Firayiministan ya ce an kashe sojoji kimanin ashirin daga cikin wadanda suka shirya juyin mulkin, kuma an shawo kan lamarin yanzu.

Mista Yildrim ya bukaci mutanen kasar da su sake daga tutocin Turkiya a garuruwa da birane da dare.