An kaddamar da fasfo din bai-daya na Afirka

Hakkin mallakar hoto au
Image caption Cikin batutuwan da za a tattauna a taron, har da batun rashin tsaro da ya addabi kasashen Afrika

An kaddamar da fasfo na bai-daya na kasashen Tarayyar Afirka, a wajen bude taron koli na kungiyar a Kigali, babban birnin Rwanda.

Shugaba Idris Deby na Chadi da Paul Kagame na Rwanda ne suka fara karban fasfodin daga Tarayyar Afrikan.

Za a bai wa shugabannin kasashen Afirka da Ministocin harkokin waje da manyan jami'an Tarayyar Afirkan na su fasfon a cikin kwanaki biyu masu zuwa da za a yi a wurin taron.

Tarayyar Afirkan na fatan zuwa shekarar 2018, kasashe za su fara bai wa sauran jama'arsu fasfon.

Manufar fasfon na bai-daya ita ce a bunkasa zirga-zirgar jama'a a tsakanin kasashen nahiyar ba tare da takura ba, da kuma bunkasa kasuwanci a tsakanin kasashen.

'Matsayar Tarayyar Afirka kan kotun ICC'

A ranar Lahadi ne shugabannin kasashen Tarayyar Afrikar suka fara taron, kuma batun dangantakar kasashen da Kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague shi ne a kan gaba.

Shugabannin da dama sun bukaci kasashen nahiyar da su kaurace wa kotun sakamakon zargin da suke yi cewa kotun na yi wa shugabannin nahiyar bi-ta-da-kulli.

Shugabannin dai sun fi son kafa wata kotu ta musamman a nahiyar Afrika wadda za ta dinga hukunce-hukuncen da suka shafi tauye hakkin bil'adama.

Shugaban Sudan, Omar Al-Bashir, wanda ya bijire wa sammacin kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague, shi ma ya isa Kigali domin halartar taron kungiyar Tarayyar Afrikan, bayan gwamnatin Rwanda ta tabbatar masa cewa ba za a kama shi ba.

Kazalika, taron na kwana biyu zai tattauna a kan rikicin Sudan Ta kudu, da kuma shirin kungiyar Tarayyar Afrika na yin fasfo na bai-daya da bai wa al'umomin 'ya'yan kungiyar damar shiga kasashen juna ba tare da takardar biza ko izini ba.