An sake harbe 'yan sanda a Amurka

Rahotanni daga Louisiana na Amurka na cewa an harbe akalla 'yan sanda biyu, ko ma fiye da haka, a wani harin bindiga da aka kai musu.

Rahotannin sun ce lamarin ya auku ne a kusa da hedikwatar 'yan sanda ta jihar da ke Baton Rouge.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce wani mutum ne, fuskarsa a rufe, ya rika harbi kan mai uwa da wabi.

Wasu rahotanni sun ce wasu jami'an 'yan sandan da dama sun jikkata.

An killace yankin da lamarin ya auku, kuma ana gudanar da bincike domin gano dan bindigar.

Zaman dar-dar ya karu tun bayan da 'yan sanda suka harbe wani bakar fata, Alton Sterling, a birnin makonni biyu da suka gabata.

Magajin garin Baton Rouge, Kip Holden ya yi kira ga jama'a da su sanya 'yan sandan cikin addu'a, sannan a yi aiki da hankali a wannan yanayi.