Kudan zuma ya tarwatsa 'yan wasa

Kudan Zuma Hakkin mallakar hoto
Image caption Kudan Zuman ya amfakawa 'yan wasa da 'yan kallo.

Garken Kudan zuma sun tarwatsa wani wasan kwallon kafa a kasar Ecuador, lokacin da suka far ma 'yan wasa da alkalai da kuma 'yan kallo da harbi ana tsakiyar wasa, lamarin da ya tilasta dakatar da wasan bayan miti goma kacal da farawa.

A jiya ne dai aka fara fafatawar tsakanin kulab din kwallon kafa na River Ecuador da takwaransa Aucas.

'Yan wasan sun saurara zuwa minti talatin ko za a samu sukunin ci gaba da wasan, amma Alkalin wasan ya ce ya dakatar da wasan zuwa yau Litinin domin a kammala shi.

An dai gayyaci 'yan kwana-kwana domin su taimaka wajen yakar kudan zuman.